• Home  
  • Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata Naira 70,000 alawus din sufuri
- Babban Labari

Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata Naira 70,000 alawus din sufuri

Gwamnatin Najeriya ta amince da riƙa biyan ma’aikata alawus na sufuri na Naira 70,000 duk wata na tsawon watanni shida, wanda zai fara daga watan Nuwamba 2026, domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziƙi. Hakan na ƙunshe ne a cikin matsayar da aka cimma a ƙarshen wani taron sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta […]

Gwamnatin Najeriya ta amince da riƙa biyan ma’aikata alawus na sufuri na Naira 70,000 duk wata na tsawon watanni shida, wanda zai fara daga watan Nuwamba 2026, domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziƙi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin matsayar da aka cimma a ƙarshen wani taron sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a ranar Talata a Abuja.

Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi ta ƙasar ta kira taron ne domin tattauna batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, bayan NLC ta buƙaci a inganta yanayin aiki da kuma ba da tallafin rage matsin tattalin arziki.

Tawagar gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Ministan Kwadago Dokta Muhammad Dingyadi, da Darakta Janar na Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, da kuma shugaban ƙungiyar ƙwadago NLC, Mista Joe Ajaero, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

Matsayar ta bayyana cewa tallafin zai shafi ma’aikata a dukkan matakai na gwamnati na tsawon watanni shida.

Taron ya kuma amince cewa za a biya alawus-alawus na watanni 19 da ma’aikatan lafiya ke bi cikin watanni uku, wanda zai fara daga watan Disamba 2026.

Dangane da batun mafi ƙarancin albashi na ƙasa, ɓangarorin biyu sun amince cewa za a kafa Kwamiti, wanda zai fara zamansa nan take.

Ɓangarorin sun kuma amince cewa za su sake haɗuwa bayan wata guda domin tantance yadda ake aiwatar da abubuwan da aka cimma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai