• Home  
  • Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.
- Babban Labari

Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.

Babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Saminu Abdullahi hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali da tarbiyya, bayan ta same shi da laifin kisan kai ba da ganganci ba. Shari’ar ta samo asali ne daga wani rikici da ya barke tsakanin Saminu da abokin kasuwancinsa, marigayi Auwalu Sulaiman, wanda daga bisani ya kai […]

Babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Saminu Abdullahi hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali da tarbiyya, bayan ta same shi da laifin kisan kai ba da ganganci ba.

Shari’ar ta samo asali ne daga wani rikici da ya barke tsakanin Saminu da abokin kasuwancinsa, marigayi Auwalu Sulaiman, wanda daga bisani ya kai ga rasa ransa.

Rahotanni sun nuna cewa a yayin takaddamar, Saminu ya dauko wata Wukar aski wato zabira , inda ya caka wa Auwalu a kafada, raunin da ya samu ya janyo masa zubar jini mai yawa, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa.

Bayan faruwar lamarin, an gurfanar da Saminu a gaban kotu bisa zargin kisan kai karkashin sashe na 221 na kundin laifuffuka na jihar Kano.

Sai dai bayan sauraron shaidu daga bangaren masu gabatar da kara da kuma bayanan wanda ake tuhuma, kotun ta yanke cewa kisan bai kasance da ganganci ba, bisa hujjojin da aka gabatar a yayin shari’ar.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya bayyana cewa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali da tarbiyya, sannan kuma zai biya iyalan marigayin diyyar Naira miliyan 10, idan kuma ya gaza biyan kudin, zai sake zaman gidan yari na tsawon shekaru 10.

Alkalin ya kuma bayyana cewa za a fara kirga wa’adin hukuncin ne daga ranar da aka kama Saminu.

A karshe, kotun ta bayyana cewa duk wanda bai gamsu da hukuncin da aka yanke yana da damar daukaka kara cikin kwanaki 90.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai