NOA ta taya kungiyar kwallon kafa ta mata ta yan kasa da shekaru 17 nasarar lashe gasar kofin duniya.
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya ’yan ƙasa da shekara 17 murnar lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA, tana mai bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga ƙasa.
Babban Daraktan hukumar, Malam Lanre Issa-Onilu, ya ce nasarar ta nuna jajircewa, haƙuri, ladabi da haɗin kai, tare da tabbatar da irin ƙwazon matasan Najeriya wajen yin fice a duniya.
Ya bayyana cewa nasarar ta wuce harkar wasanni, domin ta nuna irin damar da matasan Najeriya ke da ita wajen shawo kan ƙalubale da cimma manyan nasarori.
Issa-Onilu ya kuma ce ’yan wasan sun zama jakadun ƙasa na gari, tare da zama abin koyi ga sauran matasa wajen nuna jagoranci da kishin ƙasa.
Ya ƙara da cewa hukumar na shirin karrama ’yan wasan da jami’an tawagar ta hanyar ba su tutar Najeriya da kundin taken ƙasa.
