An hallaka mutum ɗaya, yayin da wasu biyar suka jikkata bayan wasu da ake zargin ’yan jagaliya ne sun tarwatsa wani gangamin siyasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Delta.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar a kan titin Nnebisi da ke birnin Asaba, lokacin da magoya bayan jam’iyyar ƙarƙashin ƙungiyar Obidient/OK Movement ke gudanar da wani tattakin goyon baya ga ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Bright Edafe, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, inda ya ce rundunar ta fara bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma dalilan da suka haddasa rikicin.
Ya ce tun kafin gudanar da gangamin, rundunar ta samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar tashin hankali, saboda haka ta gayyaci masu shirya taron tare da gargaɗin kada su gudanar da jerin gwano a kan tituna.
A cewarsa, rundunar ta ba su shawarar gudanar da taron a wani keɓantaccen wuri da za a iya samar musu da isasshen tsaro, amma suka yi watsi da shawarar.
