• Home  
  • Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Alhaji Aminu Dantata
- Labarai

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Alhaji Aminu Dantata

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata, matar hamshakin dan kasuwa, mai taimakon jama’a a nan Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata, matar hamshakin dan kasuwa, mai taimakon jama’a a nan Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata.

Shugaban, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, a jiya, ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tausayi da taimakon marasa galihu da kuma sha’awar hidimta wa mutane.

Ta kuma kasance mai farin jini mai son raba duk abin da take da shi ga al’umma.

Shugaban Buhari ya yi addu’ar Allah ya jiƙanta tare da karɓi ayyukanta na alheri, ya kuma bai wa iyalan Dantata hakurin jure wannan babban rashi da aka yi da ma al’ummar Musulmi bakiɗaya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai