• Home  
  • Majalisar Jihar Neja Ta 10 Ta Gayyaci Hukumomin Tsaron a Zamanta Na Farko
- Labarai

Majalisar Jihar Neja Ta 10 Ta Gayyaci Hukumomin Tsaron a Zamanta Na Farko

Sabuwar Majalisar Dokokin jihar Neja ta 10 ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin jin bahasi daga wajensu akan matsalar rashin tsaron da ke kara kamari a jihar.

Majalisar Jihar Neja Ta 10 Ta Gayyaci Hukumomin Tsaron Jihar Kan Matsalar Tsaro

Sabuwar Majalisar Dokokin jihar Neja ta 10 ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin jin bahasi daga wajensu akan matsalar rashin tsaron da ke kara kamari a jihar.

Sabon shugaban Majalisar Dokokin jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce, a yau Laraban ne za su gana da shugabannin hukumomin tsaron dake aiki a jihar wanda hakan shi ne zaman aiki na farko da za su fara yi bayan kaddamar da majalisar a jiya Talata.

A baya dai an sha zargin ‘yan Majalisun jihohin da zama ‘yan amshin shata ga bangaren gwamnoni bisa la’akkari da yadda suke zama tamkar rakumi da akala a tsakaninsu da banagaren zartarwar.

To sai dai, shugaban Majaliasar Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce a wannan karon za su hada hannu da bangaren zartarwa wajan kawo ci gaba mai amfani ga Al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai