Rashin samun daidaito game da wanda zai jagoranci majalisar jihar Jigawa karo na takwas, ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabbin ‘yan majalisar a jiya Talata.
Takaddamar ta kaure tsakanin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar cikin su har da tsohon gwamnan jihar Badaru Abubakar, dangane da zaben shugaban majalisar dokokin jihar.