• Home  
  • Kungiyar Editocin Najeriya Ta Zabi Eze Anaba Na Jaridar Vanguard a matsayin Shugaba
- Labarai

Kungiyar Editocin Najeriya Ta Zabi Eze Anaba Na Jaridar Vanguard a matsayin Shugaba

Sauran wadan aka zàba sun hada da Hussaina Akila Banshika ta Gidan Radiyo Tarayya da ke Abuja a Matsayin mataimakiyar shugaba, da  Umoru Ibrahim na Jaridar Triumph da ke aka zaba matsayin Mataimakin Shugaba shiyyar Arewa.

Eze Anaba

Kungiyar Editocin Najeriya ta zabi Eze Anaba na Jaridar Vanguard a matsayin Shugaba.

Eze ya Samu kuri’u 250 akan abokin takararsa Bolaji Adebiyi na This Day wandà ya tsira da kuri’u 81.

Sauran wadan aka zàba sun hada da Hussaina Akila Banshika ta Gidan Radiyo Tarayya da ke Abuja a Matsayin mataimakiyar shugaba, da  Umoru Ibrahim na Jaridar Triumph da ke aka zaba matsayin Mataimakin Shugaba shiyyar Arewa.

Sauran su ne  Iyobosa Uwugiaren  a matsayin Sakatare, sai Steve Nwosu a matsayin ma’ajin kungiya.

An Kuma zabi Tsohon Darektan sashen  Labarai da al’amuran yau da kullum na Gidan Talabiji na Abubakar Rimi da ke Kano Muhammad  Sanusi Jibrin matsayin memba Mai wakiltar shiyar  Arewa.

Zaben Wanda aka gudanar a Otel din Rockview da ke Owerri Jihar Imo, ya samu halartar  Editoci gidajen Jaridun kasar nan da na Gidajen Radiyo da Talabijin sama da 500 daga jihohin kasan nan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai