Home » Abubuwan Da Suke Sa Yawan Bari

Abubuwan Da Suke Sa Yawan Bari

Likitar ta ce cin abincin dake dauke da sinadarin inganta jiki, Shan maganin ‘Folic Acid, guje wa kamuwa da cututtukan sanyi, guje wa kamuwa da cutar Hepatitis musamman nau’in B da C an daga cikin matakan da ya kamata mata na kiyayewa.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Kwararriyar likitan jarirai Efunbo Dosekun ta bayyana wasu hanyoyin da mata za su kiyaye domin guje wa haihuwar bakwaini dayin ɓarin ciki.

Efunbo wacce ita ce shugaban likitocin asibitin wayar da kan mutane hanyoyin kula da jarirai da yara kanana ta bayyana haka yayin tattauna wa da maneman labara.

Likitar ta ce cin abincin dake dauke da sinadarin inganta jiki, Shan maganin ‘Folic Acid, guje wa kamuwa da cututtukan sanyi, guje wa kamuwa da cutar Hepatitis musamman nau’in B da C an daga cikin matakan da ya kamata mata na kiyayewa.

Ta ce Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO ta bayyana cewa haihuwan bakwaini ko yin ɓari na faruwa ne idan mace ta haihu yayin da cikinta ke makonni 36 ko kasa da haka.

Haihuwan bakwaini na daga cikin matsalolin dake kisan yara ‘yan kasa da shekara biyar sannan koda sun rayu sukan kamu da nakasa da dama a jikinsu.

“Kamata yayin mata su zage damtse wajen inganta lafiyar su kafin su dauki ciki da lokacin da suke da ciki domin guje wa wadannan matsalolin.

“Wasu kasashen waje kan amince wa mata su fara bai wa mata maganin frolic acid da zaran sun kai shekara 18.

“Folic acid na taimakawa wajen inganta lafiyar jariri yayin da yake cikin mahaifiyar sa musamman Kare su daga kamuwa da cututtukan spinal bifida wanda kan sa a haifi yara da nakasa a jikinsu ko kuma su mutu.

Likitan ta yi kira ga mata dake dauke da wasu cututtuka a jikinsu kamar su siga, hawan jini da sauran su da su rika zuwa asibiti domin ganin likita kafin da suke da ciki da lokacin da suke da ciki domin guje wa matsalolin da ka iya cutar da lafiyar su da dan dake cikinsu.

Efunbo ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ware kudade domin inganta lafiyar yara kanana a kasar nan tare sa ware kan mutane mahimmancin dake tattare da kula da lafiyar yara da mata masu ciki.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?