Home » Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Dagane Da Cutar Damuwa

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Dagane Da Cutar Damuwa

Cutar damuwa cuta ce da tafi addabar mata mussaman ma wadanda suke da kananun shekaru daga 18 zuwa sama Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da kalubale da dai sauransu.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

kwararren likitan kwakwalwa dake aiki a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya ce mata mussaman wadanda ke da kananun shekaru daga 18 zuwa sama sun fi kamuwa da cutar damuwa sakamakon wadansu abubbuwa da ke faruwa da su a irin wadannan shekarun.  

Ya ce, masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun bayyana cewa sau da yawa idan wani iftila’i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da kalubale da dai sauransu.

Cutar damuwa da ta shafi kwakwalwar ɗan Adam, cuta ce da ake samunta a ko ina a fadin duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Inda ta ƙara da cewa mata sun fi maza fuskantar wannan Mummunar Cutar a duniya.

Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.

Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa.

A kan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko kuma wasu ma su ce rashin haƙuri ne, ko rashin tawakkali ke haddasa ta ga wanda ya gamu da ita. Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa, da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kai.

Muhasatvr ta tattauna da wani ƙwararren likitar lafiyar ƙwaƙwalwa a nan kano, Dakta Inuwa kan matsalar kuma ya lissafa wasu alamomi da asha masu cutar na fama da su.

Babbar alama ga mai fuskantar matsananciyar damuwa asha tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili.

Sai dai masana sun ce abin da mutane asha gane ba dangane da cutar shi ne damuwa ashae kamar kowace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum.

Mutanen da suke fuskanci wani mummunan tashin hankali, cin zarafi, ko wani mummunan iftila’i na rayuwa sun fi shiga hatsarin kamuwa da matsananciyar damuwa.

Sai dai akwai hanyoyin rage kaifin cutar ko magance ta da suka hada da ba da baki da magunguna.

Ko da yake wani bincike ya tabbatar da cewa fiye da asha 75 cikin ɗari, na masu fama da matsananciyar damuwa a kasashen da ke da ƙaranci da matsakaicin kuɗin shiga, basa samun kulawar ma’aikatan lafiya.

A lamomin cutar sun hada da.

  • Yawan fargaba da saurin fushi.
  • Yanke ƙauna.
  • Daina jin daɗin abubuwan da suke faranta rai.
  • Yawan gajiya, rashin karsashi da jin cewa babu abin da ke da daɗi.
  • Kasa mayar da hankali a kan abu
  • kasa tuna abin da ya faru da gaza yanke hukunci.
  • Sauyi a yanayin barci ko na cin abinci.
  • Yawan jin ciwon jiki musamman wanda babu wata alama ta zahiri.
  • Tunanin kashe kai ko yunkurin hakan.

Ana warkewa daga cutar damuwa?

Dakta Inuwa ya ce ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya dace.

“Idan aka lura wani ya fara nuna alamomin wannan cuta, abu na farko shi ne a kai shi asibiti,”

Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.

“Muna ba da magunguna, sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wannan cuta kewa, da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu.”

Sannan ta ce makusantansu su riƙa jan su a jiki, da nuna musu kulawa.

“Duka waɗannan ne ke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya,” in ji likitan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?