Wata mata mai suna Maimunat Ibrahim ta ce likitocin asibitin Aminu Kano sun cire mata mahaifa da Jaririn ta ba tare da sanina ba.
Maimunat ta bayyana hakan ne a shirin yamma na Brekete Family na ranar Al-hamis ɗin da ta gabata, wanda Human Right Radio Abuja ke gabatarwa.
Mahaifiyar ta ce, “Na kwashe kwana kusan goma a cikin wani ɗaki da likitocin Asibitin suka kaini kafin su cire min mahaifa da jaririn da ke ciki na, kuma dika ba tare da na sani ba” Inji Maimunat
Tinda fari, Maimunat Hamza Ibrahim, wadda ‘yar asalin Kano ce ta ce, wani likita mai suna Dr. Nuhu da wata Dr. Jamila a Asibitin ne suka ce ta kwanta a kan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya bayan sun kirawota da Jaka da kuma Wawiya.
Maimunat ta kuma ƙara da cewa, har barazanar sace mata sauran ‘ya’yan da ta haifa akayi bayan ta kaisu ƙara wata hukumar ƙwatar ‘yanci matsawar ba ta daina tuhumar Asbitin na Malam Aminu Kano da sace mata mahaifa da kuma jaririnta ba.
Ta ce sai daga bayan aikuwar lamarin ne, mijinta ya ce ya bunne jaririn da ta haifa lamarin da ya ƙara damula mata lissafi, ace an binne jariri ba tare da kowa ya sani ba.
To sai dai cikin wani saƙo da hukumar gudanarwar Asibitin na Malam Aminu Kano ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ƙaryata wannan zarge-zarg da aka yi wa likitocinta, sai dai ta ce duk da haka zata ƙara zurfafa bincike.