Dakarun Rundunar Sojin Ƙasa na Nijeriya sun kashe ɗaya daga cikin ’ya’yan ƙasurgumin ɗan taadar nan, Bello Turji tare an kuma rumbun abincinsa.
Wannan na kunshe a cikin wani sako da Zagazola Makama Ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi ya wallafa ranar Asabar a shafinsa na X.
Zagazola ya ce sojojin da ke ƙarƙashin rundunar Fansar Yamma sun kai hari ta sama da ƙasa inda suka tarwatsa maɓoyar Turji a yankin Fakai da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi.
Daga cikin matsugunan ’yan ta’addan da sojojin suka tarwatsa sun haɗa da Zangon Dan Gwandi, Zangon Tsaika, Zangon Kagara da kuma wata makaranta da Turji ya mayar rumbun adana kayan abinci da makamai a jihar Zamfara.
Rahotanni daga majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Makama cewa Bello Turji da mayaƙansa sun tafka asara da ta wuce misali. Inda suka ce:
“Mun kashe ɗansa da mayaƙansa da dama a yayin harin kuma a wannan lokaci mun jiyo muryar Turji yana neman wasu jagororin ’yan bindiga bakwai da su kawo masa agaji amma babu wanda ya amsa kiran a cikinsu,” inji majiyar.