Tun bayan Iftila’in haɗarin Tankar mai da ya faru a ranar Talata a Majiya dake Jihar Jigawa, zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasu sun kai 180 a cewar wasu mazauna yankin.
Tun a ranar 15 ga watan Oktoba ne wata babbar tankar dakon man fetur tayi haɗari akan hanyar ta ta zuwa Jihar Yobe da ga Kano.
Haɗarin ya faru ne a Majiya dake ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
Inda nan take aka tabbatar da rasuwar kimanin mutane 150, sai kuma ƙarin wasu da suka jikkata.
Jihar dai na ta samun tallafi, a baya bayan nan.