• Home  
  • Gwamnonin Arewa Sun Tallafawa Jihar Jigawa Da Naira Miliyan 950
- Babban Labari - Labarai

Gwamnonin Arewa Sun Tallafawa Jihar Jigawa Da Naira Miliyan 950

Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayar da gudunmawar Naira Miliyan 950 don taimakawa iyalan waɗanda suka rasu dama waɗan da suka jikkata sakamakon faɗuwar tankar dakon man fetur a Majia jihar Jigawa. Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ne ya sanar da ba da tallafin ya yin ziyarar da su […]

Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayar da gudunmawar Naira Miliyan 950 don taimakawa iyalan waɗanda suka rasu dama waɗan da suka jikkata sakamakon faɗuwar tankar dakon man fetur a Majia jihar Jigawa.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ne ya sanar da ba da tallafin ya yin ziyarar da su ka kai don Jajantawa gwamnati dama al’ummar Jihar.

Jama’a daga da wajen Najeriya na cigaba da jajantawa al’ummar jihar Jigawa faruwar wannan ifti’ai.

A kwanakin baya ma dai al’ummar ƙauyen Nahuche da ke ƙaramar Hukumar Taura sun fuskanci ifti’ain ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

  • Jihar Jigawa na ɗaya daga cikin jihohin da ke da zaman lafiya a Arewacin Najeriya, sai dai a bana an samu mace-mace da dama sakamakon ifti’ai iri daban-daban.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai