Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya umurci wata tawagar ‘yan sanda ta yi aiki tare da hukumar zaben Najeriya, wajen bincike da kuma gurfanar da shugaban hukumar zabe na jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari.
Wanna ya biyo bayan rahoto da aka samu na cewa an neme shi Hudu Yunusa Ari an rasa, domin baya ansa wayarsa.