A ɗaya ɓangaren kuma, kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Air Peace a ƙasar nan, ya bayyana aniyarsa ta kwashe ‘yan Nijeriya da rikicin kasar Sudan ya rutsa da su kyauta, idan har gwamnatin tarayya za ta iya kai su filin jirgin sama mai aminci da tsaro, a kowacce kasa da ke makwabtaka da Sudan.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito a yau daga shugaban kamfanin kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Allen Onyema.
Ya bayyana cewa, daliban da sauran ‘yan Nijeriya wadanda suka makale a cikin kasar da ke fama da yakin, suna bukatar taimakon kamfanin cikin gaggawa.
Bai kamata ace komai gwamnati ce kadai za ta yi ba.
Onyema ya kuma kara da cewa ba sa dana sanin zama ‘yan Nigeria, saboda kalubalen da kasar ke fuskanta.
Yace, idan aka kai daliban wata kasa, kamar Kenya ko Uganda, za su shiga kasar don kwashe mutanenmu.
Wasu iyaye sun fara kira gare mu da mu taimaka. A shirye muke mu sake yin taimakon da muka saba yi,” inji shi.