• Home  
  • ADC Ta Rusa Shugabancin Jam’iyyar a Kano, Ta Kafa Kwamitin Riƙo.
- Siyasa

ADC Ta Rusa Shugabancin Jam’iyyar a Kano, Ta Kafa Kwamitin Riƙo.

Jam’iyyar ADC ta rusa shugabancinta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni. Mataimakiyar Shugabar ADC ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta sanar da hakan a ranar Litinin yayin taron […]

Jam’iyyar ADC ta rusa shugabancinta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni.
Mataimakiyar Shugabar ADC ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta sanar da hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
A cewarta, an naɗa Alhaji Umar Bala a matsayin shugaban kwamitin riƙon ƙwaryar da zai jagoranci jam’iyyar na ɗan lokaci.
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ba wai don fifita wani ɓangare ba ne.
Ta ce manufar ita ce dawo da daidaito, tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin jam’iyyar, tare da cike giɓin shugabanci da ya taso a jihar.
Ta kuma yaba wa mambobin jam’iyyar ADC a Kano bisa gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa jam’iyyar, tana mai jaddada cewa shugabancin ƙasa na ADC na matuƙar girmama jajircewarsu da sadaukarwar da suka nuna.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000