• Home  
  • Matatar Dangote ta fitar da man biliyan 757 zuwa Turai
- Kasuwanci

Matatar Dangote ta fitar da man biliyan 757 zuwa Turai

Matatar man Dangote ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757 zuwa Turai a watan Yuni. Jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5. Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne mafi yawan man da Najeriya ta taɓa fitarwa […]

Matatar man Dangote ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757 zuwa Turai a watan Yuni.

Jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne mafi yawan man da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun lokacin da matatar Dangote ta fara samar da irin wannan mai a shekarar 2024.

Haka kuma, Najeriya ta zarce Amurka wajen samar wa Turai man jirgin sama a watan Yunin inda ta fitar da tan 466,000, yayin da Amurka ta fitar da tan 399,000 kacal.

Masana sun ce wannan nasara na nuna yadda matatar Dangote ke ƙara bunƙasa fitar da kayayyakin mai daga Najeriya tare da ƙarfafa matsayin ƙasar a kasuwannin makamashi na duniya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000