• Home  
  • AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.
- Labarai

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.

Mataimakin sufeto janar na yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya Zone 1 Kano, AIG Garba Ahmed, ya jagoranci bikin bankwana tare da karrama, CP Taiwo Adedeji Abdul Mojeed, bayan samun ƙarin girma zuwa mukamin Kwamishinan yan sanda. An gudanar da bikin ne a hedikwatar Zone 1 da ke Kano, inda manyan jami’an […]

Mataimakin sufeto janar na yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya Zone 1 Kano, AIG Garba Ahmed, ya jagoranci bikin bankwana tare da karrama, CP Taiwo Adedeji Abdul Mojeed, bayan samun ƙarin girma zuwa mukamin Kwamishinan yan sanda.

An gudanar da bikin ne a hedikwatar Zone 1 da ke Kano, inda manyan jami’an rundunar da sauran abokan aiki suka halarta domin girmama shi bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake jagorantar sashen binciken manyan Laifuka na shiyyar (ZCID).

A jawabinsa, AIG Garba Ahmed ya bayyana cewa bikin na daga cikin lokutan farin ciki a rayuwarsa ta aiki, yana mai cewa CP Taiwo ya nuna ƙwarewa, tawali’u da jajircewa wajen gudanar da aikinsa.

Ya ce a tsawon lokacin da suka yi aiki tare, bai taɓa ba shi kunya ba.

Ya kuma taya sabon kwamishinan murnar ƙarin girman, tare da yi masa fatan samun nasara wajen sauke nauyin sabon mukaminsa.

Shi ma a nasa jawabin, CP Taiwo Adedeji Abdul Mojeed ya gode wa Allah bisa damar da ya samu ta hawa matakai daga ɗan sanda har zuwa kwamishinan yan sanda.

Ya kuma miƙa godiya ga iyayensa bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba shi, tare da yabawa AIG Garba Ahmed bisa jagoranci da shawarwarin da suka taimaka wajen ci gaban aikinsa.

An kammala bikin ne da miƙa wa CP Taiwo kyauta sannan aka ɗauki hotunan tarihi tare da mahalarta taron.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai