• Home  
  • Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da ƙasashen Gulf
- Kasashen Ketare

Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da ƙasashen Gulf

Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar tattaunawar diflomasiyya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a yankin Gulf. Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 108 kan kowacce ganga. A ranar Juma’ar da ta gabata, Saudiyya ta sanar da […]

Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar tattaunawar diflomasiyya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a yankin Gulf.

Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 108 kan kowacce ganga.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Saudiyya ta sanar da cewa ta rufe bututun man, bayan wasu hare-hare da Iraqi ta kai da jiragen marasa matuƙa, sun yi masa ɓarna.

Tun da farko masarautar Saudiyya ta zargi mayaƙan ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran da kai irin waɗannan hare-hare.

A ɓangare guda kuma, ƙasar Oman ta ɗage wani taro da aka shirya yi a ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawan da ke yankin Gulf domin tattauna batun mashigar Hormuz. Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai

Ba za mu dawo da tallafin

Farashin mai ya ɗaga a duniya