Alƙalin Alƙalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Halima Shamaki Mohammed, ta bayar da umarnin sakin fursunoni 88 daga gidajen gyaran hali da ke jihar domin rage cunkoso.
Daga cikin fursunonin da aka saki, 68 sun fito ne daga Gidan Gyaran Hali na Gombe, yayin da aka saki wasu 20 daga Gidan Gyaran Hali na Billiri.
An yanke shawarar sakin fursunonin ne bayan an sake duba shari’o’insu domin gano waɗanda suka cika sharuɗan da doka ta tanada na samun ’yanci.
Gidan gyaran hali na Gombe, wanda aka gina domin ɗaukar fursunoni 399, a yanzu yana ɗauke da sama da fursunoni 1,000.
Yawan fursunonin ya haifar da cunkoso tare da ƙara matsin lamba kan kayan aiki da sauran abubuwan more rayuwa a gidan.
Ana sa ran sakin fursunoni 88 zai taimaka wajen rage cunkoso da kuma inganta yanayin zaman fursunonin da suka rage a gidan.
Sake duba shari’o’in ya kuma taimaka wajen gano mutanen da suka cancanci a sake su bisa doka, amma har yanzu suke tsare.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin hukumomi na rage cunkoso a gidajen gyaran hali ta hanyar sake duba shari’o’in fursunoni lokaci zuwa lokaci da sakin waɗanda suka cancanta.
Hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa ba a ci gaba da tsare mutanen da doka ta ba su damar samun ‘yanci ba.
