Aliko Dangote ya kaddamar da babban shirin ilimi na shekaru 10 wanda zai tallafa wa dubban daliban Najeriya (musamman mata) a kowace shekara, tare da kashe biliyoyin naira, domin ba da damar ilimi ga matasa daga ko’ina cikin kasar.
Domin samun nasarar shirin, an naɗa Mai Martaba Sarkin Lafiya, Justice Sidi Dauda Bage a matsayin wanda zai jagorance shi, tare da wasu tsoffin shugabannin jami’oi da ƙwararun da suka shafi harkar ilimi.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya jinjinawa Aliko Dangote dangane da wannan aiki, ya ce har sanda ya zubar da hawaye saboda farin cikin da ya ji, la’akari da yadda Dangote ke hidima ga al’umma.
Shettima ya kuma bayyana wasu daga cikin matakan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke ɗauka na inganta bangaren ilimi da suka haɗa da tallafin karatu da inganta ilimin firamare da kuma faɗaɗa ayyukan hukumar TETFUND dake taimakawa manyan makarantu.
Mataimakin shugaban ya ce Dangote ya daɗa tinatar da su cewar, ficen da jama’a ke yi ba wai ya tsaya ne ga dukiyar da suka mallaka ba, sai dai irin gudumawar da suka bayar wajen inganta rayuwar jama’a.

