• Home  
  • Manchester United Ta Samu Ribar Kuɗi Duk Da Rashin Shiga Gasar Nahiyar Turai
- Labarai - Wasanni

Manchester United Ta Samu Ribar Kuɗi Duk Da Rashin Shiga Gasar Nahiyar Turai

Kulob din Manchester United (Red Devils) ya sanar da cewa ya samu riba na kimanin Yuro miliyan 14 (€14m) a cikin watanni uku na farkon kakar wasa (2024/2025). Wannan ci gaba ne mai nuni da kyau idan aka kwatanta da kakar wasa da ta gabata inda aka sami asarar na fiye da Yuro miliyan 7 (€7m) a daidai wannan lokacin. Duk da samun […]

Kulob din Manchester United (Red Devils) ya sanar da cewa ya samu riba na kimanin Yuro miliyan 14 (€14m) a cikin watanni uku na farkon kakar wasa (2024/2025). Wannan ci gaba ne mai nuni da kyau idan aka kwatanta da kakar wasa da ta gabata inda aka sami asarar na fiye da Yuro miliyan 7 (€7m) a daidai wannan lokacin.

Duk da samun riba, jimillar kudin shiga ya ragu da kashi 2% zuwa €141 miliyan. Dalilai biyu mafi girma sun haifar da haka

Rashin Shiga Gasar Zakarun Turai (Champions League): Kudin shiga ya ragu saboda kungiyar maza ta kare a matsayi na shida a gasar Premier, wanda hakan ya hana ta tikitin shiga gasar nahiyar Turai mai albashi.

Kudin shiga daga sayayya (retail) ya rage da kashi 9.3% zuwa €48 miliyan. Wannan saboda yarjejeniyar da kamfanin Tezos ta kare kuma ba a samu sabon mai talla da zai maye gurbinsa ba don samar da kayayyakin horo.

Rage Kudin Kasuwanci: Kudin shiga daga harkokin kasuwanci (commercial) shi ma ya ragu da kashi 1.3% zuwa €85 miliyan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai