Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta mika motoci uku dauke da giya ga hukumar Hisbah domin lalata su bayan kammala bincike.
Shugaban hukumar KAROTA, Faisal Mahmud, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Ibrahim ya fitar.
Sanarwar ta ce, motocin sun ƙunshi kwantena 410 da kwalabe 4,920 na Giya, kuma jami’an KAROTA suka cafke su yayin sintirin dare a manyan titunan birnin Kano.
- NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa
- Kotu ta yanke wa Mai Kayan Miya hukuncin kisa tare da wanke abokinsa a Kano
Mahmud ya kara bayyana cewa motocin suna kan hanya ne zuwa wurare daban-daban a cikin birnin Kano lokacin da jami’an suka tarar da su, kuma hakan ya biyo bayan bin diddigin takardun jigilar su.
Rahoton ya nuna cewa kamen ya yi daidai da aikin hukumar na gano duk wani motsi da ka iya zama haɗari ga tsaro da lafiyar jama’a, tare da ci gaba da sa ido don dakile yaduwar kayan maye a Kano.
A wajen karɓar motocin da aka kwace, kwamanda-janar na hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, wanda shugaban sashen yaƙi da Giya, Sani Nasidi, ya wakilta, ya yaba wa jami’an KAROTA kan irin kulawa da ƙwazo wajen gano su.
