Alhazan Najeriya shida sun rasu a Saudiyya, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin bugun zuciya.
Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajji, Dr Usman Galadima ne ya tabbatarwa da hakan a cikin wata tattaunawarsa da manema labarai.
A cewar galadima, Galadima mahajjatan da suka rasu sun hada da biyu daga jihar Osun, sai daya daga Kaduna da wani daya daga jihar Filato.
Ya ce, izuwa yanzu maniyyata 15,860 suka yi jinya sanadiyyar cutuka daban-daban, wadanda suka hada da mura da gyambon ciki da hawan jini da kuma cizon sauro.
inda kara da cewa sama mahajjata 100 an tura su asibitoci a kasar Saudiyya. Haka kuma wasu alhazan Najeriya 30 da aka tabbatar da cewa suna da matsalar tabin hankali an kai su asibitocin Saudiyya kuma za su yi aikin hajji saboda “yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.