Masana kiwon lafiya a fannin ingantacen abinci wato dietians sun tabbatar da cewa rake na da muhimci ga lafiyar al’umma.
Lokuta da dama mutane kan sha rake domin zaƙin da Allah ya hore masa ba tare da sanin alfanun da ruwan raken ke da shi ga lafiya ba.
Masana kiwon lafiya sun gano cewa rake na maganin cututtuka da dama da suka haɗa da cutar hanta da ƙoda, da kuma cututtuka da akan kamu da su a wajen kwanciya da magance zazzabi, har ma da mura.
Rake yana taimakawa wajen saisaita hawan jini da kuma sauran cututtuka da suka shafi jini.
Sauran alfanun da ruwan rake ke da shi kuwa sun haɗa da:
- Yana karfafa garkuwar jiki da kare mu daga kamuwa da cutar daji.
- Yana ƙara yawan ruwan da ke jiki da karfin jiki, musamman ga masu aikin ƙarfi ko aiki a cikin rana.
- Ruwan rake har wayau na taimaka wa lafiyar zuciya, da kuma Ido da kwakwalwar.
- Rake na taimakawa ƙodarmu wajen tace fitsari da kyau.
- Sai kuma gyaran fata saboda sinadarin glycolic acid da ake samu a cikinsa.
- Haka kuma bincike ya nuna cewa ruwan rake ba shi da illa ga masu ciwon sukari (sai dai ana so masu fama da Type-2 diabetes ka da su sha rake da yawa saboda larurar da suke da ita)
Da fatan zamu riƙa ta’ammali da rake domin inganta lafiyarmu