• Home  
  • Sarakunan Gargajiya 19 Sun Yi Murabus A Sokoto
- Babban Labari - Labarai

Sarakunan Gargajiya 19 Sun Yi Murabus A Sokoto

Rahotanni dake fitowa daga jihar Sakoto na cewa masu riƙe da sarautun gargajiya aƙalla 19 ne suka yi murabus domin nuna goyon bayan su ga Sanata Ibrahim Lamido Waɗanda suka ajiye muƙaman nasu sun haɗa da Dagacin Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi […]

Rahotanni dake fitowa daga jihar Sakoto na cewa masu riƙe da sarautun gargajiya aƙalla 19 ne suka yi murabus domin nuna goyon bayan su ga Sanata Ibrahim Lamido

Waɗanda suka ajiye muƙaman nasu sun haɗa da Dagacin Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi da Tudun Dankusu da Alhazzai da dai sauransu.

Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan da Dagacin garin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa yayi Murabus.

Takardar wadda ya sa wa hannu, tace, “an naɗa ni Dagacin Sabon Birni a ranar 15 ga watan Yulin 2014, kuma na ajiye muƙami na don na mara wa Sanata Ibrahim Lamiɗo baya.”

Alhaji Lauwali Shu’aibu Dagacin Taka-Tsaba ya ce, mun ajiye muƙaman mu amma ba wanda ya gayyace mu don yaji matsalar mu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai