• Home  
  • Amurka Ta Yaba Wa Najeriya Bisa Kama Jagororin Ansaru
- Babban Labari - Labarai

Amurka Ta Yaba Wa Najeriya Bisa Kama Jagororin Ansaru

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya yaba da kama fitattun shugabannin ƙungiyar Ansaru da jami’an tsaronta suka yi. A ranar Asabar ne gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaronta sun kama ƴan ƙungiyar ta Ansaru, waɗanda take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022 har suka tseratar da wasu fursunoni. Mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar […]

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya yaba da kama fitattun shugabannin ƙungiyar Ansaru da jami’an tsaronta suka yi.

A ranar Asabar ne gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaronta sun kama ƴan ƙungiyar ta Ansaru, waɗanda take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022 har suka tseratar da wasu fursunoni.

A wani rubutu da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce, “muna yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Najeriya da jami’an tsaronta bisa samun nasarar kama shugabannin ƙungiyar Ansaru da ake nema ruwa a jallo, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a da Mahmud al-Nigeri da aka fi sani da Mallam Mamuda.”

Ofishin ya ƙara da cewa kama mutanen guda biyu, “babbar nasarar ce ga ƙasar a yunƙurinta na yaƙi da ta’addanci.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000