• Home  
  • An Daure Magidanci Kan Damfarar Tsohuwar Matarsa
- Babban Labari - Labarai

An Daure Magidanci Kan Damfarar Tsohuwar Matarsa

Wata kotun Musulunci da ke jihar Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin wata biyu kan damfarar tsohuwar matarsa. Kotun da ke zamanta a ’Yan Alluna a Ƙaramar Hukumar Fagge, ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifin bai wa tsohuwar matarsa rasit ɗin bogi na kuɗin abincin ɗansu. A yayin gurfanar da […]

Wata kotun Musulunci da ke jihar Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin wata biyu kan damfarar tsohuwar matarsa.

Kotun da ke zamanta a ’Yan Alluna a Ƙaramar Hukumar Fagge, ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifin bai wa tsohuwar matarsa rasit ɗin bogi na kuɗin abincin ɗansu.

A yayin gurfanar da wanda ake zargin, ya ce a wani shago ne aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin da ya bai wa tsohuwar matar tasa.

Ya shaida wa kotun cewa, a unguwar Mandawari aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin.

Mai Shari’a Khadi Nasir Abdullahi Muhammad, ya yanke masa hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira dubu hamsin.

Ya kuma ba da umarnin yi masa bulala 10.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai