Daga Fatima Abdullahi Shadai
Matasan garin Dawaki kudu sun share babban Asibitin yankin a wani bangare na murnar shigowar sabuwar shekarar 2025.
Matasan sun kuma wanke banɗakunan asibitin tare da share wasu titunan cikin garin Dawakin kudu da ke jihar Kano.

A tattaunawar mu da ɗaya daga cikin matasan da suka yi wannan gagarumin aiki, Adamu Abdullahi ya ce a ƙalla kusan shekaru ashirin ko talatin da suka gabata ba a taɓa yin irin wannan aiki da matasa suka fito daga ma bambantan wurare ba. Ya ƙara da cewa yana kira ga matasa maza da mata da su yi koyi da su.
Daga cikin wadanda suka gudanar da wannan gagarumin aiki har da ‘yan mata, Umma Rabi’u Aminu ta bayyana cewa Sun ji daɗi sosai da mata suka fito aka yi wannan aiki da su, hakan ya nuna suna da haɗin kan da su kansu basusan suna da shi ba. Suna kira ga matasa da su haɗa kai da su yi koyi da irin aikin su don a samu ci gaba.
Shima shugaban ƙungiyar Ɗalhatu Muhammad ya yi mana ƙarin haske akan wannan aikin, inda ya ce dalilin da ya sa suka fito suka yi wannan aiki shi ne, da su fito suna wasa da ababen hawa, ko wasa da wuta, da sauran abubuwan da ka iya kawo barazana ga lafiyarsu, haka ne ya sa suka ƙirƙiri abin da za su amfanar da ƙasar su da kuma al’umma, ba zasu zauna komai ace gwamnati ce zata yi musu ba Ya ƙara da cewa Matasa suna da tasiri a cikin al’umma a dan haka matasa maza da mata su yi ƙoƙarin ko yi da su.