Dubun wasu ɓarayin yara ta cika bayan an kama su da satan yara daga jihar Taraba dake Arewa Maso Gabashin Najeriya zuwa kudu maso gashin ƙasar.
Rahotanni na cewa an ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba sakamakon wani aiki na haɗin guiwa tsakanin ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).
- Rikicin Ƙabilanci Ya YI Ajalin Sama Da Mutane 50 A Filato
- Kotu Ta Sauke Julius Abure Daga Shugabancin Jam’iyyar LP
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto ‘yan asalin ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba ne.
Misis Mary ta bayyana wa manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a cewa an yaudari yaran ne daga unguwar su aka yi safararsu zuwa jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Ta ƙara da cewa, sun gano su kuma sun ceto su a garin Aba, a Onitsha da kuma wani ɓangare na Jihar Imo.
Ta ce waɗan da suka yi safarar yaran sun ce wai yaran marayu ne.
A yayin ganawar kwamishinar da manema labarai, ta bayyana cewa, an damƙe masu aikata safarar ne a garin Gembu da ke ƙaramar hukumar Sardauna, a lokacin da suke ƙoƙarin satar wasu yaran.
Wanda sanadiyyar kama su ɗin ne aka yi nasarar ceto sauran yaran takwas, yayin da wasu da dama da aka yi safarar su ba a kai ga ceto su ba.