• Home  
  • An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar
- Babban Labari

An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar

An fitar da matar nan ta farko da aka tabbatar na ɗauke da cutar Ebola a Najeriya daga asar zuwa Switzerland domin ci gaba da jinyarta. Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, ne ya tabbatar da hakan. Yana mai cewa an fiytar da matar ne daga kasar bisa amincewarsa, inda ya ƙara da cewa mijinta, […]

An fitar da matar nan ta farko da aka tabbatar na ɗauke da cutar Ebola a Najeriya daga asar zuwa Switzerland domin ci gaba da jinyarta.

Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, ne ya tabbatar da hakan.

Yana mai cewa an fiytar da matar ne daga kasar bisa amincewarsa, inda ya ƙara da cewa mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun kamuwa da cutar ba, ya yi mata rakiya.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ya ke martani kan wani bidiyo da aka wallafa na yadda ake shiga da matar jirgin sama, ministan ya ce marar lafiyar ta samu sauƙi sosai kafin a kai ta Switzerland.

Sai dai Pate ya ce hakan ba yana nuna cewa marar lafiyar ta samu sauƙin da ba za ta iya yaɗa cutar ba, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da bin tsauraran ƙa’idojin kariyar lafiyar jama’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai