• Home  
  • An Ga Jinjirin Watan Shawwal A Saudiyya.
- Babban Labari

An Ga Jinjirin Watan Shawwal A Saudiyya.

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke alamnat kawo ƙarshen azumin watan Ramadan. Shafin Inside the Haramain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kwamitin duba watan ne ya cimma matsaya bayan ɗaukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar […]

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke alamnat kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.

Shafin Inside the Haramain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kwamitin duba watan ne ya cimma matsaya bayan ɗaukar awanni ana neman wata.

Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar ta Saudiyya.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne sakamakon kwamitin duba watan a Najeriya da sauran ƙasashe.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai