• Home  
  • Yan Sanda Sun Munsanta Labarin Kone Yan Kabilar Igbo A Kano.
- Babban Labari

Yan Sanda Sun Munsanta Labarin Kone Yan Kabilar Igbo A Kano.

  Rundunar yan sandan Jihar Kano, ta musanta labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta, cewar an kai wa wata mota mai dauke da fasinjoji ‘yan kabilar Igbo hari a Kano. Kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. A […]

 

Rundunar yan sandan Jihar Kano, ta musanta labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta, cewar an kai wa wata mota mai dauke da fasinjoji ‘yan kabilar Igbo hari a Kano.

Kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

A cewar rundunar, wannan labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, kuma bashi da tushe balle makama.

Sanarwar na zuwa ne kwanaki biyu bayan harin da aka kai wa wasu matafiya ‘yan Arewacin Nijeriya a garin  Uromi dake Jihar Edo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 16.

Tuni dai rundunar yan sanda ta kasa ta ce ta kama mutane 14 da ake zargi da hannu a wannan kisan gilla, kuma ana ci gaba da bincike.

Sanarwar ta bukaci al’umma da su guji yada labaran karya, wadanda za su iya haddasa fitina ko sanya firgici a cikin al’umma.

Rundunar ta tabbatar da cewa tana aiki tukuru domin kare lafiyar dukkan mazauna jihar ba tare da la’akari da kabilarsu ko addininsu ba.

SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa sun fara gudanar da cikakken bincike domin gano tushen labarin kanzon kuregen da ake yadawa , tare da daukar matakin doka kan wadanda suka kitsa shi.

A karshe rundunar ta bukaci al’umma da su kasance masu sanya ido da kuma kai rahotan dukkan wani abu da basu amince dashi ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai