Ƴansanda a Najeriya sun ce suna gudanar da bincike kan aƙalla mutum 28 da aka gano ƙoƙon kansu da ƙasusuwansu daga wasu sansanonin miyagu a dazuka da ke jihar Abia a kudu maso gabashin ƙasar.
An gano gawarwakin ne yayin wani samame da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia ta gudanar a yankin Isuochi na karamar hukumar Umunneochi, yankin da ya sha fama da satar mutane da sauran munanan laifuka.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Maureen Chinaka ta ce ƴansanda sun gano ƙoƙon kawuna da ƙasusuwan mutum 28 daga sansanonin da ke dazukan Umuaku da Nneato.
Masu bincike na zargin cewa ƙasusuwan na iya kasancewa na mutanen da aka sace, amma ana ci gaba da bincike domin tantance ko su wane ne da kuma yadda suka mutu.
Jami’ai daga ɓangarori daban-daban na rundunar ‘yan sanda ne suka shiga aikin, ciki har da sashen yaki da miyagun laifuka da sashen yaki da satar mutane da sashen yaki da kungiyoyin asiri, da sashen tattara bayanan sirri da sauran rundunoni na musamman.
‘Yan sanda sun ce sun kaddamar da samamen ne bayan samun bayanan sirri kan zargin ayyukan masu aikata laifi a dazukan.
A cewar kakakin, zuwa yanzu ba a kama kowa ba yayin samamen saboda waɗanda ake zargi sun tsere kafin ƴansanda su isa sansanonin.
Ƴansanda sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da kuma aka ƙara sa ido domin gano mutanen da suke tsere.
Kwamishinan ƴansandan jihar Abia Wilfred Afolabi ya ce samamen wani ɓangare ne na yaƙin da ake na tarwatsa maɓoyar miyagu da kuwa yaƙi da matsalar tsaro a jihar.
Gano ƙasusuwan na iya ƙara tayar da hankula game da ƙungiyoyin masu satar mutane da ke fakewa a dazukan da ke sassan kudu maso gabashin Najeriya, inda suke sace direbobi, matafiya da mazauna yankunan domin neman kuɗin fansa.
A shekarun baya-bayan nan, hukumomi sun gano gawarwakin da suka fara ruɓewa a samamen da aka kai kusa da kasuwar shanu da kuma ake zargin suna da alaƙa da ayyukan masu satar mutane.