An gudanar da jana’izar hamshaƙin ɗankasuwar nan na Najeriya, Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Annabi (S.A.W) da ke birnin Madina.
Jana’izar ta gudana ne bayan sallar magariba, inda kuma aka binne gawarsa a maƙabarta Baƙiyya mai tarihi a birnin na Madina.
Mutane da dama ne daga Najeriya suka halarci jana’izar – wadda aka jinkirta tun da farko sakamakon wasu dalilai na ciƙa ƙa’ida.
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ta halarci jana’izar, tare da tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi manyan jagororin jihar.




A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa manema labarai.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha’awarsa cewa “Allah ka kashe ni a wannan gari” a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.

