• Home  
  • Tsohon Ministan Shari’ar Nijeriya Abubakar Malami Ya Koma Jam’iyar ADC
- Babban Labari - Labarai

Tsohon Ministan Shari’ar Nijeriya Abubakar Malami Ya Koma Jam’iyar ADC

Tsohon ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC tare da komawa haɗakar ƙawancen jam’iyyu hamayya ta ADC. Cikin wata sanarwa da tsohon ministan ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya ce ya ɗauki matakin ne domin bayar da tasa gudunmowa wajen ceto Najeriya daga durƙushewa. Abubakar Malami ya […]

Tsohon ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC tare da komawa haɗakar ƙawancen jam’iyyu hamayya ta ADC.

Cikin wata sanarwa da tsohon ministan ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya ce ya ɗauki matakin ne domin bayar da tasa gudunmowa wajen ceto Najeriya daga durƙushewa.

Abubakar Malami ya bayyana dalilan rashin nuna halin ko’ina kula da gwamnatin APC ke yi wa matsalolin da suka addabi Najeriya.

”Zubar da jini ya yi yawa, ga matsalar tsaro da ke addabar yankunanmu musamman arewaci da ke fama da ƴanfashi da masu garkuwa da mutane da matsalar ta’addanci, amma duk da waɗannan, gwamnatin APC ta fifita siyasa maimakon kare rayukan ƴanƙasa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Tsohon ministan ya kuma zargi gwamnatin APC da haifar da tashin farashin kayyaki, musamman na abinci da rashin ayyukan yi, amma duk da haka ya ce gwamnati a mayar da hankalinta kan siyasa.

Abubakar Malami – wanda ɗan jihar Kebbi ne daga arewa maso yammacin Najeriya – ya zargi gwamnatin Tinubu da aiwatar da naɗe-naɗe don siyasa ba don ci gaban ƙasa ba.

”Wanna ne dalilin da ya sa na shiga ADC, domin haɗa ƙarfi wuri guda da nufin kawar da wannan gwamnati, domin samar da sabuwar tafiya da za ta inganta rayuwar ƴan Najeriya”, in ji shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000