Gwamnatin Gombe ta haramta sana’ar bola jari a duk faɗin jihar, bisa abin da ya kira barazanar tsaro da kuma zargin sana’ar da ƙarfafa ayyukan laifi.
An yanke wannan shawara ne a wani taron Majalisar Tsaro na musamman da gwamnatin jihar ta gudanar tare da manyan jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, domin ƙarfafa zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnatin ta bayyana cewa bincike da rahotannin hukumomin tsaro sun nuna cewa harkar bola-jari na taimakawa wajen satar kadarorin gwamnati da na jama’a, ciki har da wayoyin lantarki, bututun ruwa, kayan aikin gwamnati da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa — abin da ke ƙara ta’azzara matsalolin tsaro a jihar.
A cewar gwamnatin, haramcin zai fara aiki nan take, yayin da aka kafa kwamitin aiwatarwa da sa ido domin tabbatar da bin dokar a dukkan ƙananan hukumomi na jihar.
- ’Yan Ta’addar JNIM Sun Kashe Shugaban Ƙaramar Hukumar Torodi a Nijar
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta lashi Takobin hana masu yunkurin aikata laifuka sakat.
Haka kuma, an umarci jami’an tsaro da su ɗauki tsauraran matakai kan duk wanda aka samu da karya wannan doka, tare da ƙara sintiri a muhimman wurare.
Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa tsaro shi ne ginshiƙin ci-gaba, kuma cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk wani mataki da ya dace domin kare martabar jihar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ba hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai masu amfani, yayin da gwamnati ke duba hanyoyin samar da madadin sana’o’i da shirye-shiryen tallafi, musamman ga matasa da suka dogara da harkar bola domin rayuwa
