Home » An Kama 420kg Na Fatar Dabbar Pangolin A Kano- Hukumar Kwastam.

An Kama 420kg Na Fatar Dabbar Pangolin A Kano- Hukumar Kwastam.

Sun yi kammen ne a wani samame na haɗin gwiwa da jami’an leƙen asiri suka gudanar a wata unguwa da ke cikin birnin kano.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Hukumar kwastam ta Najeriya reshen Kano da jigawa, ta kama fatar dabbar Fangoli,

wata dabba mai kama da Kada wadda in ta razana take dunƙulewa tamkar ƙwallo domin kare kai,  mai nauyin kilogiram 420.

Sun yi kammen ne a wani samame na haɗin gwiwa da jami’an leƙen asiri suka gudanar a wata unguwa da ke cikin birnin kano.

Shugaban hukumar kwastom shiyyar Kano da Jigawa Abubakar Dalhatu ne ya bayyana hakan a ranar alhamis yayin ganawa da manema labarai a kan.

Kwanturola Dalhatu Abubakar, ya ce anyi kaman ne ranar laraba da misali karfe 7 na dare,

sakamakon wata haɗin gwiwa da jami’an ofishin kula da namun daji na kwastam, da na hukumar leƙen asiri, da kuma  ‘yan sandan kwastam.

Abubakar ya kuma sanar da cewa an kama wani mutum ɗaya da ake zargi da safarar namun daji ba bisa ka’ida ba, kuma a halin yanzu yana tsare shi don ci gaba da bincike.

Kwanturoli Dalhatu Abubukar ya ja kunnen masu fataucin cewa ba za a amince da aikata laifukan saɓawa dokar kare namun daji ba, a jihar Kano, dama Najeriya, baki daya.

Abubakar ya ce matakin ya yi daidai da dokar hukumar kwastam ta Najeriya ta shekarar 2023,

Musamman sashe na 55 (c) wanda ya umarci hukumar ta aiwatar da dokokin da suka shafi kare nau’o’in da ke cikin hadari da kuma kare halittu masu rai.

Kwanturolan ya kuma amince da goyon bayan abokan huldar kasa da kasa, da suka hada da ofishin hulda da leken asiri na yankin (RILO) da kuma Focus Conservation, saboda ci gaba da hadin gwiwarsu wajen yaki da laifukan namun daji.

Daga karshe ya yabawa kokarin jami’an kwastam, musamman ma ofishin kula da namun daji na musamman, bisa kwarewa da kwazon da suke yi na aiki.

“Ina kuma nuna matukar godiya ga Kwanturola-Janar na Kwastam na kasa, wanda shugabancinsa ke ci gaba da karfafa ayyukanmu,

Abubakar ya tabbatar da cewa hukumar za ta kara sanya ido tare da tura kayan aikin fasaha don yaki da safarar namun daji yadda ya kamata.

Jami’in na NCS ya kara da cewa, “Hakinmu ne na hadin gwiwa don kare wadannan nau’ikan da ke cikin hadari ga al’ummomi masu zuwa.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?