Gwamnatin Najeriya ta ce ana sa ran rukunin farko na ‘yan Najeriya da ake kwashe daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi (xenophobia) za su isa ƙasar a safiyar ranar Alhamis.
A wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar ranar Laraba, ya ce waɗanda za a kwashe za su tashi daga Afirka ta Kudu ne a daren Laraba.
Ma’aikatar ta ce kamfanin jiragen sama na Air Peace ne zai gudanar da aikin jigilar mutanen, yayin da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen aikin.
Sanarwar ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati, ta hannun ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa, ta shirya dukkan matakan karɓa da tallafa wa waɗanda za su dawo.
Ya ce bayan isowarsu za a yi musu rijista da tantancewa tare da ba su tallafin da ya dace kafin a haɗa su da iyalansu.
Tashin hankali ya ƙaru a Afirka ta Kudu bayan wata ƙungiya da ke adawa da baƙin haure marasa takardu ta buƙaci dukkan baƙi waɗanda ba su da izinin zama su fice daga ƙasar kafin ranar 30 ga Yuni.
Kasashen Ghana da Mozambique sun riga sun kwashe ɗaruruwan ‘yan ƙasarsu, yayin da Malawi da Najeriya suka sanar da shirinsu na yin hakan.
