A jiya ne aka gurfanar da Donald Trump a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan.
Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don ka da ta yi bayani game da alaƙar da ta taɓa shiga tsakaninsu lokacin da yake takarar shugabancin ƙasar a zaben 2016.
Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taɓa kamawa a tarihin kasar.
Sai dai a lokuta da dama Trump ya sha musanta wannan zargi da ake masa.
Tare da bayyana cewa duk waɗanna tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon ƙasa.