Dan jaridar da ake zargi da caccakar Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya jawo masa rasa aikinsa sakamakon harzuka da Gwamnan ya yi.
Rahotanni sun ce dan jaridar, mai suna Malam Adamu Ngulde da ke aiki a wani gidan rediyo mai zaman kansa da ake ce da shi Al-Ansar cikin Jihar ya karbi takardar dakatarwar ne daga mahukuntan tashar.
Takardar ta ce an sallame shi daga aiki ne sakamakon korafin da Gwamnan ya yi a kan caccakarsa da Adamu Ngulde ya yi a cikin wani shirin sa da ake ce da shi ‘Arewa ina mafita’.
Wasu rahotanni na cewa, Gwamna Zulum ya yi ikirarin cewa a cikin shirin ne dan jaridar ya caccaki Gwamnatinsa ba tare da yi masa adalci ba musamman ta wajen rashin kokarin duba lamarin kamar yadda tsarin aikin jarida ya tanada.
Majiyarmu ta tuntubi dan jaridar kan matakin sallamar tasa, inda ya bayyana cewa abincinsa ne ya zo karshe a gidan, kuma ya rungumi kaddara.
Sai dai daga bisani, sabuwar kafar yaɗa labarai ta kasar Turkiyya TRT ta ba shi aiki a matsayin wakilinta mai kula da Jihohin