• Home  
  • An kama masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da ɓarayin dabbobi a Jigawa
- Babban Labari

An kama masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da ɓarayin dabbobi a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami, sata da kuma satar shanu a sassa daban-daban na jihar. ’Yan sandan sun kuma ce sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47, babura da kuma dabbobin da aka sace yayin wasu samame da suka gudanar tsakanin 22 zuwa 29 […]

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami, sata da kuma satar shanu a sassa daban-daban na jihar.

’Yan sandan sun kuma ce sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47, babura da kuma dabbobin da aka sace yayin wasu samame da suka gudanar tsakanin 22 zuwa 29 ga watan Mayu, 2026.

Kakakin rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya ce nasarar ta samu ne ta hanyar aiki da bayanan sirri ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Haruna A. Yahaya.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai wasu uku da ake zargi da fashi da makami a yankin Hadejia.

An kuma gano bindiga ƙirar AK-47 a gidan ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin.

A wani samame kuma, ’yan sandan sun daƙile shirin garkuwa da mutane a Jihar Bauchi, inda suka kama mutane biyu da ake zargi.

Haka kuma, an kama wasu da ake zargi da satar tumaki da shanu a ƙananan hukumomin Gwaram da Taura, inda aka ƙwato dabbobin da aka sace da kuma babur da ake amfani da shi wajen aikata laifin.

A yankin Ringim kuma, ’yan sandan sun wargaza wata ƙungiyar ’yan fashi da ke kafa shingen ƙarya don tare motocin masu wucewa, inda aka kama mutane uku.

Rundunar ta kuma ce ta ƙwato wasu babura da aka sace a wasu samame daban-daban.

’Yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike, kuma ana sa ran ƙara kama wasu masu hannu a laifuffukan.

Kwamishinan ’Yan Sandan, CP Haruna A. Yahaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka a jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai