• Home  
  • An kama wani matashi kan yunƙurin baiwa ɗaurarru tabar wiwi a cikin burodi a Kano
- Babban Labari - Labarai

An kama wani matashi kan yunƙurin baiwa ɗaurarru tabar wiwi a cikin burodi a Kano

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), reshen jihar Kano ta bayyana cewa jami’an ta da ke aiki a gidan gyaran hali na Gwauron Dutse sun cafke wani matashi bisa yunƙurin bada tabar wiwi ga ɗaurarru a jihar A sanarwar da Kakakin NCoS, CD Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar a yau Alhamis a Kano, an […]

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), reshen jihar Kano ta bayyana cewa jami’an ta da ke aiki a gidan gyaran hali na Gwauron Dutse sun cafke wani matashi bisa yunƙurin bada tabar wiwi ga ɗaurarru a jihar

A sanarwar da Kakakin NCoS, CD Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar a yau Alhamis a Kano, an kama matashin mai suna Muhammad Kabir dan unguwar Hotoro Tishama da tabar wiwi din kunshe a cikin burodi.

A cewar CSC K/Nassarawa, an kama matashin ne a harabar babbar kotun jiha yayin da ya ke yunkurin baiwa ɗaurarru wiwi bayan an kawo su kotun domin yi musu Shari’a.

Kakakin ya ce tuni dai Kwantarola na NCoS na Kano, Ado Inuwa ya bada umarnin miƙa matashin zuwa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai