Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta bayyana shirin kafa rundunonin wayar da kan jama’a kan kyawawan ɗabi’u a dukkan jihohi 36 na ƙasar da babban birnin tarayya Abuja.
Darakta-Janar na hukumar, Malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan a wani taron shugabannin gudanarwar hukumar da aka gudanar a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jami’an hukumar daga jihohi 36 da Abuja, da daraktocin shiyyoyi shida na Najeriya da kuma shugabannin jami’an wayar da kan al’umma.
Ya ce hukumar za ta kuma gudanar da gangamin wayar da kan jama’a da ilimantar da masu zaɓe na tsawon makonni shida a faɗin ƙasar nan, domin ƙara wayar da kan ‘yan ƙasa kan muhimman batutuwan ƙasa da kuma zaɓe.
Shugaban hukumar Mallam Issa-Onilu ya buƙaci ma’aikatan hukumar da su ƙara ƙaimi wajen yaɗa saƙonnin wayar da kai ta kafafen sada zumunta, tarukan al’umma da kuma hulɗa kai tsaye da jama’a.
Ya kuma bayyana shirin hukumar na samar da na’urar sa ido kan kafafen yaɗa labarai, domin bibiyar yadda ake watsa shirye-shiryenta da saƙonnin wayar da kai a gidajen rediyo da talabijin da kuma jaridu a faɗin ƙasar nan.
A wani ɓangare kuma, Daraktar kula da ma’aikata ta hukumar, Misis Ayisola Olowoyo, ta bayyana cewa an fara shirye-shiryen gudanar da jarabawar ɗaukaka matsayin ma’aikata, wadda aka tsara yi a ranar 12 ga Janairu, tare da sanar da hukumar shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB).
Haka kuma, Daraktar shiyyar Kudu maso Gabas, Misis Theresa Madueke, da Daraktar hukumar ta Jihar Anambra, Misis Ifeoma Chijioke, sun yaba wa Darakta-Janar kan ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da hukumar da kuma inganta ayyukanta.
Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka haɗa da wayar da kan al’umma kan zaɓe tun daga tushe, amfani da fasahar sadarwa wajen hulɗa da ‘yan ƙasa da kuma rawar da hukumar za ta taka a matsayin mai sa ido a babban zaɓen 2027.

