• Home  
  • An kammala tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran
- Babban Labari

An kammala tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran

Tawagar manyan jamai’an Iran da Amurka sun yi zaman tattaunawar sulhu ta sa’o’i biyu a birnin Islamabad. Ba a sanar da matsayar zaman ba, amma wakilin BBC ya ce amincewar bangarorin biyu su yi ganawar kai tsaye alama ce ta nasara. Kafar yaɗa labaran Iran ta ce za a ƙara wata tattaunawar a ƙarshen mako. […]

Tawagar manyan jamai’an Iran da Amurka sun yi zaman tattaunawar sulhu ta sa’o’i biyu a birnin Islamabad.

Ba a sanar da matsayar zaman ba, amma wakilin BBC ya ce amincewar bangarorin biyu su yi ganawar kai tsaye alama ce ta nasara.

Kafar yaɗa labaran Iran ta ce za a ƙara wata tattaunawar a ƙarshen mako.

Wakilan Amurka ba su ce komai ba game da zaman tattaunawar sulhun.

Ɓangarorin biyu na zargin juna da karya yarjejejniyar tsagaita wuta.

Ya yinda suke neman matsaya game da batutuwa da dama da suka haɗa da wucewa ta mashigin Hormuz da janyewa Iran takunkumai da tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon da kuma makomar shirin nukiliyar Tehran.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai