• Home  
  • An rantsar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun wa’adi na biyu
- Babban Labari

An rantsar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun wa’adi na biyu

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke, wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Osun. An yi bikin rantsuwar ne a ranar Juma’a, inda alkalin alkalai na jihar Osun, mai shari’a Adepele Ojo ta jagoranci rantsar da gwamnan a filin wasa na Osogbo City Stadium, tare da mataimakinsa, Yarima Kola Adewusi. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, […]

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke, wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Osun.

An yi bikin rantsuwar ne a ranar Juma’a, inda alkalin alkalai na jihar Osun, mai shari’a Adepele Ojo ta jagoranci rantsar da gwamnan a filin wasa na Osogbo City Stadium, tare da mataimakinsa, Yarima Kola Adewusi.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa wajen bikin, a madadin shugaba Bola Tinubu.

A cikin jawabin da ya gabatar bayan rantsuwar kama aiki, Adeleke ya bayyana sake zaɓensa a matsayin “nasarar muradin al’umma”.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan faɗaɗa ayyukan more rayuwa, bunƙasa masana’antu, sauya fasalin noma, bunƙasa tattalin arzikin zamani, yawon buɗe ido, da kuma ci gaban matasa da mata a wa’adinsa na biyu.

Gwamnan ya yi alƙawarin sauya tattalin arzikin jihar daga wanda ya dogara da ma’aikatan gwamnati zuwa cibiyar masana’antu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000