• Home  
  • Sojojin Guinea-Bissau sun ƙara wa’adin mulki zuwa shekaru biyu
- Kasashen Ketare

Sojojin Guinea-Bissau sun ƙara wa’adin mulki zuwa shekaru biyu

Hukumomin mulkin sojin da suka ƙwace iko a Guinea-Bissau sun ƙara wa’adin mulkinsu da wasu shekaru biyu, matakin da ke ƙara nuna yadda shugabannin soji a ƙasashen Afirka ta Yamma ke tsawaita zaman su a kan mulki. Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta sojin ƙasar, Manjo Janar Horta Inta-a, ya fitar da wata doka a ranar […]

Hukumomin mulkin sojin da suka ƙwace iko a Guinea-Bissau sun ƙara wa’adin mulkinsu da wasu shekaru biyu, matakin da ke ƙara nuna yadda shugabannin soji a ƙasashen Afirka ta Yamma ke tsawaita zaman su a kan mulki.

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta sojin ƙasar, Manjo Janar Horta Inta-a, ya fitar da wata doka a ranar Alhamis, inda ya ɗage zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa daga ranar 6 ga watan Disamban 2026 zuwa 26 ga watan Nuwamban 2028.

A cewar Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta sojin ƙasar, an ɗauki matakin ne saboda rashin isassun kayan aiki da kuɗaɗe, da kuma wasu muhimman sharuɗa na fasaha da ake buƙata domin gudanar da sahihin zaɓe.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake cika shekara guda da juyin mulkin sojin da ya hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embaló.

A watan Oktoba ne Firaminista Ilídio Vieira Té ya nuna cewa babu isassun sharuɗan gudanar da zaɓen da aka tsara yi a watan Disamba.

Jam’iyyun siyasa sun gaza cika wa’adin ranar 6 ga watan Oktoba na gabatar da sunayen ‘yan takararsu.

Sai dai ƙungiyoyin adawa sun ce rufe ofisoshin jam’iyyunsu da kuma hana gudanar da tarukan siyasa ne suka hana su yin hakan.

Hukumomin sojin sun ce suna buƙatar ƙarin lokaci domin shirya zaɓen.

Sai dai masu sukar matakin na ganin cewa suna son amfani da lokacin ne wajen ƙarfafa ikon da suka ƙwace, musamman bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar a wani zaɓen raba gardama da aka gudanar a watan Agusta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000