’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.

