Daga Safiyanu Haruna Kutama
Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren Juma’a.
An gudanar da Jana’izar ne a Masallacin idi na Game Village dake garin Bauchi.
Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi dai ya rasu yana da Shekaru 68.
ya bar ‘ya’ya 38 da jikoki da Dama Kuma matan sa 3.
- Dokta Hakeem Baba Ahmed Ya Ajjiye Mukamin Da Gwamnatin Tinubu Ta Bashi
- Turji Ya Kusa Komawa Ga Mahallici — Sojoji
Manyan Yan siyasa irin su tsohon matemakin shugaban Nigeriya Atiku Abubakar da kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunna JIBWIS da sauran manyan malamai tuni suka fara aikewa da sakon ta’aziyya tare da alhinin rasuwar sa.